Use APKPure App
Get Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline - Part 2 of 2 old version APK for Android
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline - Parte 2. Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
Assalamu alaikum wa rahmatullah,
Team Abyadapps ke kawo muku karatun Littafin Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 OFFLINE tare da Sheikh Jaafar Mahmud Adam. Wannan manhajja itace ta biyu wato PART 2 kuma bata bukatar a kunna data domin tayi aiki. Sauketa kan wayoyinku kawai daga nan zatayi aiki ko da ba'a kunna data ba. Works perfectly Offline.
A cikin wannan app na Siffatus Salatin Nabiyyi mp3 offline zaku ji karatun littafin (Sifat Salat Nabiy Hausa) a inda mawallafin littafin Muhammad Nasirudden Al Albani yayi bayanin yadda sallar manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) take tun daga kabbarar-harama zuwa sallama kamar kana Kallon Annabi yanayin sallar.
Don haka, akwai bukatar kowanne musulmi ya saurari wannan karatu domin kokarin kyautata babbar bauta wacce Allah subhanahu wataala yafi so wato Sallah.
A takaice littafin SIFFATUS SALATIN NABIYYI littafine na koyon yadda sallar manzon Allah (s.a.w) take.
Mai Fassara littafin cikin wannan manhajja shine Sheikh Jaafar Mahmud Adam. Allah ya gafartawa Sheikh Nasiruddeen Al Albani kuma Allah ya gafartawa Sheik Jafar Mahmud Adam.
Allah ya datar damu da sauraran karatun wannan littafi ya kuma fahimtar damu sannan ya bamu ikon yin aiki da karatun da mukaji aameen.
Idan kunji dadin wannan manhajja, kada ku manta kuyi rating dinta tauraro biyar cikin wannan gida sannan kada a manta ayi sharing da sauran yanuwa musulmai Hausa.
Bayan wannan manhajja ta siffatus salah akwai sauran manhajjoji muhimmai da wannan team ya kawo muku kamarsu: Guzurin Mahajjata bayanin yadda akeyin aikin Hajji tare da sheikh Jafar Mahmud Adam.
Domin samun manhajjoji sautin sunnah sak toh sai a rika duba catalog na team abyadapps.
Idan akwai wani tsokaci, shawara ko wani bayani da kukeson aikawa wannan team to zaku iya yin hakan ta cikin wannan manhajja. Zamu karanta kuma mu aiko muku da amsa in shaa Allahu.
Bissalam ku huta lafiya.
Last updated on Mar 30, 2019
Minor bug fixes and improvements. Install or update to the newest version to check it out!
Caricata da
蔡胜楠
È necessario Android
Android 4.1+
Categoria
Segnala
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline - Part 2 of 2
3 by Abyadapps
Mar 30, 2019